IQNA

Za A Bude Masallacin Quds Bayan karamar salla

22:57 - May 19, 2020
Lambar Labari: 3484813
Tehran (IQNA) kwamitin kula da harkokin masallacin Quds ya sanar da cewa za a bude masallacin bayan karamar salla.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a yau kwamitin kula da harkokin masallacin Quds ya gudanar da zama, inda ya  sanar da cewa za a bude masallacin bayan karamar salla ba da jimawa ba.

Bayanin ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa an kiyaye matakai na kiwon lafiya, inda har yanzu ake ci gaba da kula da masallacin tare da yin feshi a cikinsa.

Kwamitin ya kara da cewa, bayan karamar salla zai zauna tare da jami’an kiwon lafiya domin jin shawararsu kan yiwuwar bude masallacin ga masallata, kuma matukar suka bayar da shawara kan cewa babu wani hatsari, to za a bude masallacin.

Tun kimanin watanni biyu da suka gabata ne aka daina gudanar da salloli na jumaa da kuma nay au da kullum a cikin masallacin quds, domin kaucewa kamuwa da cutar corona.

 

https://iqna.ir/fa/news/3900189

captcha