IQNA

23:45 - May 23, 2020
Lambar Labari: 3484827
Tehran (IQNA) shugaban kasa Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, kasarsa a kowane lokaci tana kokarin ganin an samu tabbatar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

Shugaba Rauhani ya bayyana haka ne a wata zantawa da ta gudana a tsakaninsa da sarkin kasar Qatar Tamim Bin Hamad ta wayar tarho, bayan da sarkin na Qatar ya tuntube shi domin tattaunawa kan wasu batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Rauhani ya sheda wa sarkin Qatar cewa, alaka tsakanin Iran da Qatar tana nan daram, kuma za su ci gaba da kara bunkasata musamman a bangarori na kasuwanci da habbaka tattalin tsarki, da kuma yin aiki tare a bamgaren tsaro.

Ya kara da cewa, a kowane lokaci Iran tana kokarin ganin an samu tabbatar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya, duk kuwa da tsokanar da take fuskanta daga Amurka, amma yana fatan Amurka ba za ta sake tafka wani kure a kan kasar ta Iran ba.

A nasa bangaren sarkin kasar Qatar Tamim Bin Hamad ya mika sakon murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da yin fatan alhairi ga dukkanin musulmi a wanann lokaci da ake gudanar da bukukuwan salla.

Haka nan kuma ya sheda wa shugaba Rauhani cewa, kasarsa tana iyakacin kokarinta domin ganin an samu kwanciyar hankalia  gabas ta tsakiya, kuma za ta ci gaba da yin aiki tare da Iran a dukkanin bangarori na tattalin arziki da tsaron yankin gabas ta tsakiya.

3901027

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Iran ، Qatar ، sarkin ، shugaban kasar iran ، Hassan Rauhani ، tattalin arziki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: