IQNA

Pakistan Ta Yi Alawadai Da Gina Wurin Bauutar Hundus A Masallaci a India

23:52 - May 28, 2020
Lambar Labari: 3484844
Tehran (IQNA) Ggwamnatin kasarPakistan yi Allawadai da gina wurin bautar Hindus a masallacin musulmi a kasar India.

Shafin yada labarai na WAN ya bayar da rahoton cewa,

A'isha Farooki kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan, ta bayyana cewa matakin da gwamnatin India ta dauka na mayar da masallacin musulmi zuwa wurin bautar Hindus da cewa abin Allawadai ne.

Ta ce a daidai lokacin da duniya ta shagaltu da yaki da cutar corona, gwamnatin India kuma ta shagaltu da nuna wa musulmi wariya tare da tauye hakkokinsu a matsayinsu na 'yan kasa.

Bayanin ya ce, gina wurin bautar Hindus a kan masallaci ya kara tabbatar da irin mawuyacin halin da musulmi ske ciki a kasar India.

Kimanin watanni bakawai da suka gabata ne kotun kasar India ta yanke hulkunci kan mayar da wani masallacin muslmi zuwa wurin bauatar Hindus, tare da bayar da umarnin  bai wa musulmi wani wurin na daban domin gina wani masallacin.

 

 

 

 

 

 

3901635

 

captcha