Shafin yanar gizo na kwamitin musulmin kasar Amurka ya bayar da bayanin cewa, a cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, ya bayyana yin amfani da karfi da ‘yan sanda suke yi kan fararen hula masu zanga- zanga da cewa abin Allawadai ne.
Bayanin ya ce matakin da ‘yan sanda suka dauka tun daga farko da aka fara zanga-zangar lumana bayan kin George Flyd, na yin amfani da dukkanin karfinsu wajen murkushe masu zanga-zangar, shi ne babban abin da jefa kasar cikin halin da ta samu kanta a ciki a yanzu.
Haka nan kuma bayanin kwamitin musulmin kasar ta Amurka ya yi ishara da cewa, akwai wadanad suke yin amfani da zanga-zangar domin aikata ba daidai ba, amma dai ‘yan sanda su ne musabbabin faruwar hakan.