IQNA

Syria Ta Murkushe Wani Harin Ta'addancin Isra'ila

23:47 - June 05, 2020
Lambar Labari: 3484864
Tehran (IQNA) Rahotanni daga Siriya na cewa makamman garkuwa kan hare haren sama na kasar, sun sake murkushe wani harin yahudawan mamaya na Isra’ila.

Kamfanin dilancain labaren Siriya ya rawaito cewa, makamman garkuwa na kasar sun murkushe wasu jerin hare haren jiragen yakin sojin Isra’ila a cikin daren jiya a yankin yammacin Hama.

Kamar yadda wata majiyar soji ta shaida wa kamfanin dillancin labaran na Syria ta ce an kakkabo dayewa daga cikin makamman masu linzami da makiya suka harbo, daga cikin sararin samaniyar kasar Lebanon.

A cewar SANA, dakarun sojojin saman Syria, sun yi nasarar dakile wasu jerin hare haren makamai masu linzami da aka shirya kaiwa birnin Masyaf dake tsakiyar lardin Hama.

Wannan shine hari na baya bayan nan cikin jerin hare haren da Isra'ila ta sha kaddamarwa a yankunan sojoji na kasar Syria.

 

3903018

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yankunan sojoji ، kasar Syria ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :