IQNA

Fitaccen Dan Wasan Kwallon kafa Ya Saka Karatun Kur’ani A Motarsa

23:02 - June 07, 2020
Lambar Labari: 3484872
Tehran (IQNA) Muhammad El-neny fitaccen dan wasan kwallon kafa na kungiyar Arsenal ya saka karatun kur’ani mai tsarki a motarsa yana saurare.

Shafin yada labarai na Sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, El-neny ne ya saka wannan faifan bidiyo da kansa a cikin shafinsa na twitter.

Ya saka karatun kur’ani na Mushar Rashid Alafasi makarancin kur’ani dan kasar Kuwait ne.

Muhammad Elneny wanda ya kasance fitaccen dan wasa dan asalin kasar Masar, ya bayyana cewa a halin yanzu ya dakatar da wasa ne saboda yaduwar cutar corona.

 

3903190

 

captcha