IQNA

Sakamakon kisan da 'yan sandan kasar Amurka suka yi George Floyd bakar fata a garin Minneapoli, kimanin kwanaki 12 da suka gabata, irin wannan zanga-zanga ta barke a wasu kasashen duniya, da suka hada da Jamus, Faransa, Holland, Austria, Burtaniya, Lithuania, Mexico, Brazil, Japan, Canada, Koriya ta kudu, Australia, Mali, Tunisia, Turkiya, da sauransu, kuma har yanzu wannan zanga-zanga na ci gaba da gudana.