IQNA

‘Yan Boko Haram Sun kashe Mutane Da Dama A Borno

23:55 - June 10, 2020
Lambar Labari: 3484880
Tehran (IQNA) rahotanni daga Nigeria sun ce ‘yan Boko Haram sun kashe mutane da dama a Borno.

Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 59 ne suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan dake kiran kansu reshen kungiyar (IS) a yammacin Afrika, suka kai a wani kauyen makiyaya a arewa maso gabashin Najeriya.

Mayakan na kungiyar ta ISWAP, sun auka wa kauyen ne na Felo, dake lardin Gubio a jihar Borno jiya da rana, kamar yadda ‘yan kato da gora da kuma wakilan yankin suka shaida wa masu aiko da rahotanni.

Bayanai sun ce harin na daukan fansa ne daga mayakan bayan kisan wasu daga cikinsu da ‘yan kato da gora dake tsaron dabobinsu sukayi.

Wannan ba shi ne karon farko ba da makayan na ISWAP, da suka raba gari da kungiyar boko haram, ke kaddamar da hari ba a lardin na Gubio, dake nisan kilomita 80 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

 

 

3904055

 

captcha