IQNA

23:53 - June 12, 2020
Lambar Labari: 3484886
Tehran (IQNA) shugaba Rauhani na Iran ya bayyana cewa kasarsa na da burin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar Iran da Rasha suna da nauyi a wuyansu na tabbatar da tsaron yankin Gabas ta tsakiya, yana mai cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarori don cimma hakan da kuma sauran batutuwa.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne cikin wata wasikar da ya aike wa takwararsa na kasar Rashan Vladimir Putin don taya shi da kuma al’ummar kasar Rasha murnar zagayowar ranar kasa ta kasar Rashan inda ya ce lalle cikin shekarun baya-bayan an samu karin kyautatuwar alaka tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa a nan gaba ma alakar za ta kara karfafuwa.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa kasashen Iran da Rasha suna da wasu manufofi da suka yi tarayya cikinsu wadanda kuma za su sanya su yin dukkanin abin da za su iya wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin, yana mai cewa a halin yanzu akwai tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin bangarori biyu don cimma wadannan manufofi.

Daga karshe dai shugaba Rouhani yayi fatan alheri ga shugaba Putin da kuma al’ummar kasar Rashan.

 

 

3904304

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: