IQNA

Masar Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Al’ummar Falastinu

23:55 - June 12, 2020
Lambar Labari: 3484887
Tehran (IQNA) Masar ta jaddada goyon bayanta ga al’ummar Falastinu.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Samih Shukri ministan harkokin wajen kasar Masar ya jadadda cewa babu ja da baya kan batun goyon bayan al’ummar Falastinu.

Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya bayyana hakan ne a zaman gagagwa da kungiyar kasashen musulmi ta gudanar  ta hanayar hotunan yanar gizo, kan batun shirin Isra’ila na mamaye sauran yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Ya ce batun Falastinu lamari ne da ke bukatar daidaiton baki a tsakanin dukkanin kasashen musulmi, domin su yi magana da harshe daya na kin amincewa da wanann shiri na Isra’ila.

Haka nan kuma ya bukaci sauran kasashen musulmi da s taimaka ma al’ummar Falastinu a cikin wannan mawuyacin hali na bullar cutar corona.

Daga karshe ministan harkokin wajen na Masar ya ce suna goyon bayan matsayar da gwamnatin Falastinawa ta dauka na yin sayin daka kan hakkokin al’ummar Falastinu da kuma yin watsi da shirin na Isar’ila wanda yake a matsayin wani sabon mulkin mallaka a kan al’ummar ta Falastinawa.

3904262

 

 

 

captcha