IQNA

‘Yan Bindiga Sun Tsanata Hare-Hare A Arewacin Najeriya

22:36 - June 14, 2020
Lambar Labari: 3484894
Tehran (IQNA rahotanni daga Najeriya ‘yan bindiga suna ci gaba da kaddamar  hare-hare a yankunan arewa maso yammacin kasar.

Rahotannin sun ce sama da mahara Hamsin ne a jiya Asabar suka zagaye kauyen Mazoji da ke Karamar Hukumar Matazu, sannan kuma Maharan suka kashe mai garin.

Wannan lamari ya auku ne bayan wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar a garin ‘Yantumaki da ke Karamar hukumar Danmusa.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a garin na Mazoji da misalin karfe biyu na dare, sun kuma shafe sa’o’i suna cikin garin kafin su kashe mai garin.

Haka nan wasu daga cikin mazauna garin na Mazoji sun sheda cewa, , tun daga karfe biyu na dare har zuwa safiyar jiya  Asabar ‘yan bindigar suna cin karensu babu babbaka a cikin garin, ba tare da wani jami’in ‘yan sanda ko soja ya zo domin kawo wa al’ummar garin dauki ba.

Wannan dai na daga cikin abubuwan da suke faruwa na rashin tsaro a cikin jihar katsina da arewa maso yamma a Najeriya a cikin wadannan lokuta, lamarin da kan yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane da asarar dukiyoyi masu tarin yawa.

 

3904848

 

captcha