IQNA

MDD Ba ta Amince da Shirin Isra’ila Na Mamaye Yankunan Yammacin Kogin Jordan Ba

23:04 - June 16, 2020
Lambar Labari: 3484900
Tehran (IQNA) masana kwarru kan hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya sun yi watsi da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, masana kan harkokin doka da kuma kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, sun kalubalanci shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan tare bayyana shi da cewa ya saba wa doka.

A zaman da masanan suka gudanar sun yi dubi akn matsayin shirin an Isra’ila ta fuskar doka, inda suka yi ittifakin cewa shirin ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa.

A bangaren hakkokin al’ummar falastinu kuwa, sun bayyana shirin da cewa yana a matsayin danne hakkokin al’ummar Falastinu.

A kan haka sun sanar da cewa za su mika mahangarsu ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya domin daukar matakin taka wa Isra’ila burki kan batun.

 

3905343

 

 

captcha