IQNA

Alkalin Alkalan Falastinu Ya Gargadi Isra’ila Kan keta Alfarmar Masallacin Aqsa

22:50 - June 17, 2020
Lambar Labari: 3484904
Tehran (IQNA) Muhammad Alhabash alkalin alkalan Falastinu ya gargadi Isra’ila kan keta alfarmar masallacin aqsa.

Kamfanin dilalncin labaran Bahrain ya habarta cewa, a yau Muhammad Alhabash alkalin alkalan Falastinu ya fitar da wani bayani, wanda a cikinsa ya gargadi Isra’ila kan keta alfarmar masallacin aqsa da kuma yunkurin rusa wannan wuri mai alfarma, ta hanyar gina ramuka a kofar Magariba.

Ya ci gaba da cewa, wannan aiki da Isara’ila ta kirkira yana da nufin haifar da babbar matsala ne ga masallacin aqsa mai alfarma, domin kuwa ramukan da ake ginawa karkashin masalalcin a kowane lokaci za su iya yin sanadiyyar ruftawarsa.

Haka nan kuma alkalin alkalan na Falastinu ya kirayi sauran bangarori na duniya da su sanya baki a cikin wannan lamari, domin kuwa batu ne da ya shafi wurare masu tsarki da mabiya addinai daban-daban suke giramamawa.

Baya ga haka kuma wurare ne wadanda hukumar UNESCO ta saka su cikin wurare na tarihi.

 

3905436

 

captcha