IQNA

22:57 - June 18, 2020
Lambar Labari: 3484905
Tehran (IQNA) shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ya yi marhabin da gabatar da batun sulhu tsakanin falastinawa.

Shafin yada labarai na Falestine ya bayar da rahoton cewa, Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ya yi marhabin da gabatar da batun sulhu tsakanin Falastinawa, wanda hakan zai taimaka matuka wajen daidaita lamurra a tsakanin dukkanin bangarorin.

Bayanin ofishin shugaban kungiyar ta Hamas ya ce, bijiro da wannan batu yana da muhimmanci musamman a wanann lokaci, wanda al’ummar falastinu ke bukatar hadin kai domin fuskantar kalubalen da ke a gabansu.

Shirin dai yana da nufin hada kan dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya da ma na siyasa da ma masu mulki, domin daukar matsaya guda kan batun shirin Isra’ila na mamaye yankunan yammacin kogin Jordan.

 

3905496

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shirin Isra’ila ، mamaye yankunan ، yammacin kogin Jordan ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: