IQNA

23:54 - June 22, 2020
Lambar Labari: 3484916
Teharn (IQNA) Dakarun hadin gwiwa na kasar Iraki sun fara kaddamar da wasu hare-hare kan wasu wuraren buyar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda na Daesh a cikin lardin Salahuddin.

Dakarun hadin gwiwa na Iraki da suka hada da sojoji da kuma dakarun sa kai na al’ummar kasar Hashd Al-sha’abi, sun fara kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan wuraren buyar ‘yan ta’addan daesh a cikin lardin Salahuddin da ke iyakar kasar da Syria.

Farmakin zai hada da sauran yankunan da ke cikin lardunan Dayali, Karkuk da kuma Samirra, da nufin dakile yunkurin da ‘yan ta’addan suke yi na neman sake dawowa da karfinsu a cikin wadannan yankuna.

A daren jiya dakarun sa kai na al’ummar Iraki sun harba wasu makaman roka a kan wani sansanin ‘yan ta’addan Daesh da ke cikin yankin Samirra, bayan samun bayanai na sirri kan yadda ‘yan ta’addan suke kai komo a wurin.

3906339

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sansanin ، yankuna ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: