IQNA

Tarayyar Turai T Soki Mamayar Yankunan Falastinawa Da Isra’ila Ke Yi

23:48 - June 24, 2020
Lambar Labari: 3484925
Tehran (IQNA) ‘yan majalisar kungiyar tarayyar turai sun gargadi Isra’ila dangane da hankoronta na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dilancin labarai na maa cewa, fiye da ‘yan majlaisar kungiyar tarayyar turai dubu daya ne dagta cikin 1080 suka amince da kudirin da ke gargadin Isra’ila a kan duk wani yunkuri na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Bayanin ya ce abin da Isra’ila take neman aiwatarwa yana da matukar hadari, kuma abin da zai biyo bayan hakan ba abu mai kyau a gare ta ba, da kuma makomar siyasarta a yankin gabas ta tsakiya.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar tarayyar turai ta bayyana matsayinta na kin amincewa da wannan manufa ta Isra’ila, duk kuwa da matsin lambar da Amurka take yi a kan daidaikun kasashen turan na su amince da hakan.

 

3906688

 

 

 

 

captcha