IQNA

An Tono Wasu Dadaddun Duwatsu Da Suke Dauke Rubutun Larabaci A Makka

23:07 - June 25, 2020
Lambar Labari: 3484926
Tehran (IQNA)  an tono wasu dadaddun duwatsu da suke dauke da rubutun larabci a Makka.

Shafin yada labarai na Sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, wani akmfani mai gudanar da ayyukan kwangila ya tono wasu duwatsu na suke  a kasa daruruwan shekaru a Makka, daya daga cikin duwatsun rubutun da ke kansa yana komawa zuwa ga shekaru kimanin 655, da kuma wadanda suke komawa zuwa lokacin sarakunanan Abbasiyawa.

Muhammad Bin Abdullah Alquwais daya daga cikin manyan jami’ai na birnin Makka ya halarci wurin da aka tono duwatsun a makabartar Almu’allah da ke wajen birnin Makka, inda ya karbe su domin mika su ga bangaren adana kayan tarihi na birnin.

Kamfanin da yake aikin dai ya saba tono ababe na tarihi masu kima a yayin aikin nasa a yankunan Makka da kewaye.

 

3906653

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: komawa ، birnin Makka ، gudanar da ayyuka ، ، halarci ، tarihi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha