IQNA

Gargadi Ga Larabawa Masu Kulla Sabon Makircin Rusa Kasar Yemen

22:51 - June 29, 2020
Lambar Labari: 3484937
Tehran (IQNA) Babbar kungiyar malaman addinin musulunci ta duniya ta gargadi kasashen larabawan da suke hankoron ganin sun tarwatsa kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar malaman addinin muslunci ta duniya Muhyiddin Qari Dagi ya fadi yau cewa, akwai masu son mayar da kasar musulmi ta Yemen ta zama kasa mafi tabarbarewa a duniya.

Ya ce abin ban takaici ne yadda kasashen musulmi da ya kamata su taimaka ma al’ummar kasar Yemen, suka kasance su ne masu yaki da kasar Yemen da nufin ragargazata saboda wata tsohuwar gaba ta jahiliyya.

Ya bayar da misalin kisan kiyashin da wasu kasashen larabawa suke yi wa al’ummar Yemen, tare da jefa kasar cikin matsanancin hali na yunwa da talauci, da rashin tabbas, baya ga killacewar da ake yi wa kasar tare da hana shigar da kayan abinci da magunguna.

Dangane da yadda kasashen Saudiyya da UAE suke watandar yankunan kudancin Yemen a tsakaninsu kuwa, ya bayyana hakan da cewa abu ne mai muni matuka, maimakon hada kan al’ummar kasar, sai kasan larabawa suka shagaltu da mamaye yankunan kasar Yemen tare mayar da su tamkar yankunan kasashensu, tare da rarraba kan al’ummomin wadannan yankuna da suka mamaye.

Ya ce wannan abin kunya ne da tarihi ba zai manta da shi ba, kamar yadda kuma Allah zai yi hisabi a kan hakan.

3907535

 

 

captcha