Shafin radioalgeri.dz ya bayar da rahoton cewa, ministan ma’aikatar da ke kula da harkokin addini na kasar AljeriaYusuf Bilmahdi ya bayyana cewa, an bude ajujuwan kur’ani na bazara a kasar Aljeriya ta hanayar yanar gizo domin amfanin ‘yan makaranta, wanda kuma zai fara aiki daga wannan mako.
Ya ce wannan karatu dai ba sabon lamari ba ne, a kowace sekara ana yi, amma a bana saboda matsalar cutar corona ya zama wajibi a dauki matakai, wanda hakan ne yasa aka mayar ad shirin ta hanyar yanar gizo.
Daga cikin abubuwan da za a mayar da hankali kansu a wannan karatu akwai tilawa da kuma sanin kaidoji da hukuncin karatun kaur’ani, wanda malamai za su koyar.
Ministan ya kara da cewa, yanzu haka an fara gudanar da wannan shiri a lardin Wahran a matsayin gwaji.