IQNA

Hamas Allawadai Rahotannin Karya Da Tashar Alarabiyyah Ta Saudiyya Ta Bayar a Kanta

19:59 - July 15, 2020
Lambar Labari: 3484987
Tehran (IQNA) Hamas ta yi Allawadai da wani rahoton tashar Saudiyya da ke kokarin aibata kungiyar ta Hamas.

Kungiyar ta Hamas ta bayyana wani rahoto da tashar talabijin din ‘al’arabiyya” ta Saudiyya ta watsa na cewa daya daga cikin shugabannin kungiyar ta gwgawarmayar ya gudu zuwa Isra'ila da cewa, parpaganda ce irin ta cibiyoyin tsaron ‘yan sahayoniya.

Kungiyar ta Hamas ta ce; kafar watsa labarun ta Saudiyya tana jagoranta parpaganda ta batunci da gurbata sunan gwagwarmayar al’ummar Palasdinu, domin kashe zukatan mutane akan dogaro da gwagwarmaya

Bayanin na kungiyar Hamas ya ci gaba da cewa; Tashar talabiji din ta Saudiyya tana dogaro da karya da kirkirar abinda bai faru ba da aiki ne na jami’an leken asirin Isra'ila .

Kungiyar ta Hamas ta kuma kara da cewa; Abin da wannan tasha ta ‘al’arabiyya’ take yi, ya mayar da ita zama cikin sahu guda da ‘yan mamaya wanda yana da sakamako a tare da shi

Tashar talabijin din ‘al-arabiyya’ ta watsa wani rahoto da ke cewa; Hamas ta kame wasu ‘ya’yansa da ta samu da yi wa Isra'ila leken asirin, sannan kuma wani daga cikin shugabannin kungiyar ya gudu daga Gaza zuwa wajen ‘yan sahayoniya dauke da bayanan sirri da su ka shafi rundunar Qassam bangaren soji na Hamas.

 

3910591

 

 

 

 

captcha