IQNA

19:39 - July 18, 2020
Lambar Labari: 3484995
Tehran (IQNA) lauyoyin sheikh Ibrahim Zakzaky sun bukaci da a sake shi da mai dakinsa sakamakon matsalolin da suke fama da su.

A wata zantawa da ya yi da tashar press tv, Mas’ud Shajareh shugaban kwamitin kare hakkokin musulmi a kasar Burtaiya ya bayyana cewa, lauyoyin sheikh Ibrahim Zakzaky sun bukaci da a sake shi da mai dakinsa sakamakon matsalolin da suke fama da su na rashin lafiya.

Shajare ya ci gaba da cewa, ya zanta da lauyoyin da suke kare sheik Zakzaky da mai dakinsa, inda suka sheda masa cewa  sun bukaci kotu da ta sake su, kasantuwar suna da rashin lafiya, ga kuma halin da ake ciki na cutar corona.

Ya ce tun bayan kama shi a karshen shekara ta 2015, a cikin shekara ta 2016 kotu ta bayar da umarnin a saki Sheikh Zakzaky tare da maidakinsa malama Zinat har ma da biyansu tara ta kudi.

Haka nan kuma ya kara da cewa, yanzu haka an sanya ranar 30 ga watan Yuli da muke ciki ta zama ranar sauraren bahasi kan batun da lauyoyin suka gabatar na neman a saki shi da maidakinsa.

3911046

 

Abubuwan Da Ya Shafa: zama ، watan Yuli ، neman ، shekara ، kudi ، sheikh Zakzaky
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: