IQNA

Yahudawa Sun Aukawa Falastinawa Masu Nuna Kin Amincewa Da Rusa Makabartar Musulmi

17:56 - July 20, 2020
Lambar Labari: 3485003
Jami’an tsaron yahudawan sahyuniya sun aukawa Falastinawa masu jerin gwanon kin amincewa da rusa makabartar musulmi a  garin Yafa.

Jaridar yahudawan Isra’ila ta Yadiut Ahranut ta bayar da rahoton cewa, daruruwan jami’an tsaron yahudawan sahyuniya sun aukawa Falastinawa masu jerin gwanon kin amincewa da rusa makabartar musulmi a  garin Yafa da ke kusa da tel aviv.

Rahoton ya ce Falastinawan sun fito domin nuna rashin yardarsu da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na rushe wanann makabarta mai tsohon tarihi ta Is’af a garin Yafa.

Jaridar t ace jami’an tsaron yahudawan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu gangamin, inda aka kame wasu daga cikinsu tare da jikkata wasu.

Wannan makabarta dai tana daga cikin makabartun tarihi na musulunci, inda aka gina ta daruruwan shekaru da suka gabata, kuma tun daga lokacin ana bizne gawawwakin msuulmi ne, amma yanzu Isra’ila ta rusa ta, kuma ta fara yin gine-ginen gidaje a wurin a kan kabrukan musulmi.

 

 

3911460

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi
captcha