Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa an dauki kwararan matakai na hana yaduwar corona a yayin shigar mahajjata birnin Makka.
Maniyyata a aikin hajjin bana sun isa birnin Makka a cikin kwararan matakai na hana yaduwar cutar corona a lokacin gudanar aikin hajji, duk kuwa da cewa an takaita adadin da bai wuce mutume dubu daya da za su gudanar da aikin hajjin ba.