IQNA

Saudiyya Ta Ce Ba A Samu Cutar Corona Tsakanin masu Gudanar Da Aikin Hajji Ba

14:16 - July 31, 2020
Lambar Labari: 3485038
Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa, ya zuwa dai ba a samu bullar cutar corona tsakanin masu gudanar da aikin hajji ba.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa ba a samu bullar cutar corona tsakanin masu gudanar da aikin hajji bat un lokacin da aka fara aikin hajji har zuwa yanzu.

Shekarar bana sakamakon bullar cutar corona, mahukuntan kasar saudiyya sun kayyade adadin masu gudanar da aikin hajji wanda shi ne mafi karanci a tarihi, wanda kuma an dauki matakin ne domin kaucewa kamuwa ko kuma yada cutar corona.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Saudiyya ta sanar da cewa a cikin kasar mutane dubu 2 da 945 da suka samu saukin cutar, wanda hakan ya sa jimillar mutanen da suka samu sauki ya kai dubu 228 da 569.

A halin yanzu adadin wadanda suka suka kamu da cutar corona a Saudiyya ya kai dubu 272 da 590, yayin da kuma wadanda suka rasa rayukansu adadinsu ya kai dubu 2 da 816.

 

3913651

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya ، adadin ، dubu ، cutar corona ، aikin hajji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha