IQNA

20:54 - August 08, 2020
Lambar Labari: 3485067
Tehran (IQNA) an gudanar da taron tunawa da zagayowar idin ghadir a hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin najaf na Iraki.

Shafin yada labarai na naba ya bayar da rahoton cewa, a yau, wasu daga cikin mabiya tafarkin ahlul bait sun gudanar da kwarya-kwaryan taro a cikin hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf domin tunawa da zagayowar lokacin Ghadir.

A bisa ga al’ada dai a irin wanann lokaci miliyoyin jama’a ne suke taruwa domin rawa wanann rana ta hanyar gudanar da taruka, da kuma yin jawabai kan matsayin wanna rana a cikin addinin muslucni.

A shekarar bana sakamkon matsalar cutar corona wannan yasa dole aka takaita tarukan sabanin yadda aka saba yia  kowace shekara.

Kafin wanann lokacin cibiyar ad ke kula da hubbaren ta sanar da cewa ba za a gudanar da duk wani taro ba saboda tsoron bullar cutar corona, amma duk da haka an bar wasu mutane kadan domin gudanar da wannan taro.

 

3915381

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mabiya tafarkin ahlul bait ، birnin Najaf ، tunawa ، taruwa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: