IQNA

Gwamnatin Aljeriya Na Kokarin Bunkasa Harkokin Kudi Bisa Tsarin Muslunci

22:51 - August 17, 2020
Lambar Labari: 3485095
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Aljeriya ta sanar da sabon tsarinta na bunkasa harkokin bankin musulunci a kasar.

Shafin yada labarai na The Malaysian Reserve ya bayar rahoton cewa, gwamnatin kasar Aljeriya ta fara daukar matakai na karfafa harkokin bankin musulunci a kasar, sakamkon rahoton asusun lamuni na duniya, da ke cewa tattalin arzikin kasar zai ragu da kashi 5.2 a cikin wannan shekara.

Daya daga cikin fitattun masana harkokin tattalin arziki na kasar Aljeriya Farfesa Muhamad Budujal ya bayyana cewa, bisa la’adari da cewa lamurra da dama suka shafi bankia  kasar sun yi hannun riga da tsarin musulunci, a kasar da ke da mutane miliya 43 kuma musulmi, yin amfani da tsarin bankin musulunci a kasar zai samu karbuwa.

Ya kara da cewa, idan aka yi la’akari da cewa tsarin biyan kudin ruwa da bankuna suke amfani da shi kusan ko’ina a duniya da hakan ya hada har da Aljeriya, ya sabawa shari’ar addinin musulunci, baya ga haka kuma yin amfani da kudaden jama’a wajen gudanar da harkoki da suka sabawa shari’ar addini, kamar cinikin naman alade da ko kasuwanci giya da bankuna ke yi, wanda babu shi a cikin tsarikin bankin musulunci.

Firayi ministan kasar Aljeriya Abdulaziz Jarrad ya bayyana cewa, sakamakon bullar cutar corona, da kuma faduwar farashin danyen mai a kasuwanninsa na duniya, hakan ya  yi tasiri a kan tattalin arzikin Aljeriya, inda rashin aikin yi ya karu da kashi 15 cikin dari a kasar.

3917073

 

 

captcha