Azantawarsa da kamfanin dillancin labaran kasar Jamus Sheikh Muhammad Hussain babban malami mai bayar da fatawa a birnin Quds ya bayyana sallar jami’an gwamnatin hadaddiyar daular larabawa a cikin masallacin Quds da cewa haram ce saboda sun amince da halascin mamayar masallacin mai tsarki da yahudawa ke yi.
Ya ce tun a cikin shekara ta 2012 ya bayar da fatawar cewa, sauran musu;mi da ba su amince da halascin mamayar masallacin quds da yahudawan Isra’ila ke yi ba, sallarsu ta inganta a cikin masallacin, amma musulmin da suka amince da halascin wannan mamaya a hukuance, suna zaion cewa suna yaudarar Allah ne, saboda haka sallarsu shekaraa cikin masallacin bata lokacinsu ne kawai.