IQNA

Musulmi A Kasar Newzealand Sun Saka Furanni A Masallatan Birnin Christ Church

19:24 - August 28, 2020
Lambar Labari: 3485126
Tehran (IQNA) musulmia kasar Newzealand sun saka furanni a masallatai da ke cikin birnin Christ Church na kasar.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau Juma’a  musulmi a kasar Newzealand sun saka furanni a masallatai da ke cikin birnin Christ Church na kasar domin nuna farin cikinsu da hukuncin da kotu ta yake kan dan ta’addan da ya kashe musulmi a birnin.

Jamal Foda limamain masallacin Nur, ya bayyana cewa musulmi sun gamsu da hukuncin da kotun kasar Newzeland ta yanke a kan dan ta’addan da ya kai wa musulmi hari a cikin masallacin Nur, kuma wannan shi ne adalcin da suke jira dag akotu.

A ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2019 ne dai wani dan ta’adda dan kasar Australia mai tsananin kiyayya da musulmi, ya bude wutar bindiga a cikin masallacin Nur, ya kashe muuslmi 51 da jikkata wasu 49.

Kotun kasar Newzealand ta yanke masa hukuncin daurin rairai ba tare da karbar beli ko fitar da shi bisa kowane irin sharadi ba, inda zai mutu a cikin gidan kaso.

3919601

 

 

 

captcha