IQNA

Baharain Ta Ki Amincewa A Gudanar Da Zaman Kasashen Larabawa Da Falastinu Ta Bukata

23:18 - September 03, 2020
Lambar Labari: 3485147
Tehran (IQNA) kasar Bahrain ta yi watsi da bukatar da gwamnatin Falastinawa ta gabatar na neman kungiyar kasashen larabawa ta gudanar da zama kan batun kulla alaka da Isra’ila da wasu ke neman yi.

Tashar almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yunkurin da wasu kasashen larabawa ke na tilasta Falastinu ta amince da gwamnatin yahudawan Isra’ila, kasar Bahrain ta yi watsi da bukatar da gwamnatin Falastinawa ta gabatar na neman kungiyar kasashen larabawa ta gudanar da zama kan batun yunkurin da wasu larabawan ne kulla alaka da Isra’ila.

Rahoton ya ce ta sanar da cewa bat a amince a gudanar ad duk wani taro na kasashen larabawa  a kan wannan batu ba.

Gwamnatin Falastinu dai ta bukaci kasashen larabawa su gudanar da zama, sannan su tattauna kan batun yunkurin kulla alaka da Isra’ila, tare da neman a yi Allawadai da hakan.

Baharain ta yi wa Falastinu barazana kan cewa, idan har ta ci gaba da neman a yi Allawadai da kulla alaka da Isra’ila, to ita kuma za ta gabatar da wani kudiri a majalisar kasashen larabawa, domin a sassauta kudirin day a hana kulla alaka da Isra’ila.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da larabawan yankin tekun Fasha suka fara bayyanawa a fili kan cewa ba su da matsala da Isra’ila, inda hadaddaiyar daular larabawa ta fara kulla wannan alaka, kuma ana zaton cewa Bahrain za ta bi sahunta nan ba da jimawa ba.

3920698

 

captcha