IQNA

22:37 - September 04, 2020
Lambar Labari: 3485149
Tehran (IQNA) kungiyar malaman musulmi ta duniya ta bayyana kulla hulda da kasashen larabawa ke yi da Isra'ila a matsayin wata babbar kyauta ta Trump ga Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhyiddin Qaredaghi ya  bayyana kulla hulda da Isra'ila da wasu kasashen larabawa ke ta hankoron yi  a matsayin wata babbar kyauta ta Trump ga gwamnatin yahuwaan Isra'ila.

Ya ce duk da cewa tun daga lokacin da aka kafa Isra'ila ya zuwa yanzu, gwamnatin Amurka ita ce mai baiwa Isra'ila kariya da kuma daukar nauyinta, amma gwamnatin Donald Trump ta yi wa Isra'ila hidimar da babu wata gwamnati a Amurka da ta yi irin wannan hidima, domin tabbatar da cewa Isra'ila ta kammala mamaye Falastinu baki daya.

Malamin ya bayar da misalin cewa, gwamnatin Trump ce ta amince da birnin Quds a hukumance a matsayin babban birnin Isra'ila, kamar yadda kuma ta mika mata yankin Golan na Syria, tare da bata damar mamaye sauran yankunan Falastinawa da suke yammacin kogin Jordan.

3920816

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mamaye Falastinu ، tabbatar da cewa ، gwamnatin Amurka ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: