IQNA

22:57 - September 06, 2020
Lambar Labari: 3485156
Tehran (IQNA) babban malamin mabiya addinin kirista na Arthodox a birnin Quds ya bayyana halin da al’ummar gaza suke ciki da cewa ya munana matuka.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, babban malamin mabiya addinin kirista na Arthodox a birnin Quds Ata’allah Hanna ya bayyana halin da al’ummar gaza suke ciki da cewa yana kara munana.

Ya ce a kowace rana yana samun kira ta hanyar wayar tarho daga mutane daban-daban daga yankin zirin gaza, suna sanar das hi irin mawuyacin halin da suke ciki, sakamakon kullace su da gwamnatin yahudawan Isra’ila take yi na tsawon shekaru.

Ya ce nauyi ne day a rataya a kan dukkanin al’ummomin duniya musamman musulmi da kiristoci da larabawa da sauran masu ‘yanci na duniya, kan su taimakawa al’ummar yankin zirin gaza, domin kubutar da su daga mamaya da zaluncin gwamnatin yahudawan Isra’ila.

 

3921249

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: zirin gaza ، musulunci ، kiristoci ، taimakawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: