IQNA

Mutane Uku Sun Rasa Rayukansu A Wani Harin Ta’addanci A Yau Juma'a A Somalia

23:51 - September 11, 2020
Lambar Labari: 3485173
Tehran (IQNA) mutane uku ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin ta’addanci a Somalia.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, an kaddamar da wani harin ta’addanci na kunar bakin wake a yau a garin Kismayo da ke kudancin Somalia.

Rahoton ya ce akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu wasu fiye da 20  kuma suka jikka sakamakon wannan harin na ta’addanci wanda aka kai a wani masallaci.

Daya daga cikin jami’an gwamnati kuma babban darakta na hukumar bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya na yankin Shafi Rabi Kahen yana daga cikin wadanda suka samu munanan raunuka yayin kai wannan hari.

Babu wata kungiya da ta sanar da alhakin kai harin, amma dai ana nuna yatsun tuhuma a kan kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-shabab dai kai harin.

 

3922269

 

 

captcha