Shafin yada labarai na Almisrawi ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke sanya ido kan kyamar musulmi a nahiyar turai da ke karkashin kulawar cibiyar Azhar ta yi Allawadi da kakkasar murya kan kona kur’ani a da wasu suka yi kasar Sweden.
Bayanin cibiyar ya ce, abin masu kyamar musulunci a kasar Sweden suka yi abin Allawadai ne, kum ako alama wannan ba ‘yancin fadar albarkacin baki ba ne, cin mutunci ne a kan mabiya addinin musulunci da ke alaka ta akidar kyamar musulmi.
Cibiyar ta ce tana kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan da suka dace domin kawo karshen irin wannan aiki na batunci da cin zarafi da kuma tozarci ga musulmi.
Yan sandan kasar dai sun ce suna gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru kafin daukar duk wani mataki kan batun.
3922510