IQNA

Iran Ta Mayar Da Martani Kan Kulla Alaka Tsakanin Bahrain Da Yahudawa

23:21 - September 12, 2020
Lambar Labari: 3485178
Tehran (IQNA) Jamhuriyar musulinci ta Iran ta ce kasar Bahrain ta bi sahun masu goyan bayan laifufukan da Isra’ila ke aikatawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan yarjejeniyar kulla alaka da Isra’ilar ta sanar cimmawa da Bahrain a jiya Juma’a.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar, ta ce mahukuntan Bahrain, yanzu sun shiga jerin masu goyi bayan laifufukan mahukuntan ‘yan sahayoniya, wanda hakan babbar barazana ce ga tsaro a yankin da kuma al’ummar musulmi.

Iran ta kuma ce Isra’ila, ta kwashe gomman shekaru, ba abin da ta ke illa haddasa tashe tashen hankula da fituntunu, da kisan kai, da yake yake da zubar da jinin al’ummar Falasdinu wadanda ake ci gaba da zalunta a yankin.

Bahrain dai ta zama kasa ta biyu a yankin tekun fasha da ta kulla alakarta da Isra’ila a kasa da wata guda bayan wacce Israilar ta cimma da Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma yanzu ita ce kasar Larabawa ta hudu bayan Masar   da kuma Jordan.

 

3922330

 

captcha