IQNA

Majalisar Dokokin Iran Ta Yi Tir Da Kulla Alaka Tsakanin Bahrain Da Isra'ila

22:57 - September 13, 2020
Lambar Labari: 3485180
Tehran (IQNA) Kwamitin kula da harkokin siyasar waje da kuma tsaron kasa a majalisar dokokin kasar Iran, ya yi tir da Allawadai da matakin da gwamnatin Bahrain ta dauka na kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

A zaman da kwamitin ya gudanar, ya bayyana wannan mataki da cewa, ba wanu abu ba ne illa yunkurin kawar da batun al’ummar Falastinu tare da mantawa da hakkokinsu da yahudawan sahyuniya suka kwace musu tare da taimakon manyan kasashe masu girman kai.

Bayanin ya ce abin kunya ne ga sarakunan larabawan da suka mika kai ga siyasar yahudawan sahyuniya, kuma suka amince da su zama ‘yan amashin shata masu dakon wannan siyasa da kuma aiwatar da ita a kan al’ummar musulmi da larabawa.

Iran dai ta bayyana irin wannan mataki da larabawan tekun fasha suke dauka na mika kai ga yahudawa a matsayin wani babba abin kunya na tarihin musulmi da larabawa, inda suka saryar da hakkokin ‘yan uwansu falastinawa saboda karfafa siyasar Trump domin ya ci zabe mai zuwa a Amurka.

Tun kafin wanna lokacin dai jami’an Isra’ila sun sha bayyana cewa suna da alaka ta tsawon shekaru tsakaninsu da sarakunan larabawan yankin tekun fasha, sun sha ganawa da wadannan sarakuna a cikin kasashen saudiyya, Bahrain, da kuma hadaddiyar daular larabawa.

 

3922570

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tsawon shekaru Kulla Alaka Tsakanin
captcha