IQNA

21:58 - September 14, 2020
Lambar Labari: 3485184
Tehran (IQNA) babbar jami’ar majalisar dinkin duniya kan harkokin da suka shafi kasar Iraki ta gana da Ayatollah Sayyid Ali Sistani.

Kamfanin dillancin labaran Furat News ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya kan harkokin da suka shafi kasar Iraki Jeanine Hennis-Plasschaert, ta gudanar da tattaunawa tare da Ayatollah Sistani a gidansa da ke birnin Najaf na kasar Iraki, inda suka tattauna batutuwa da dama tare da shi.

Ta ce tattunawarta da Ayatollah Sistani ta yi armashi matuka, inda suka tabo batotuwa da suka shafi zaben ‘yan majalisa da za a gudanar a kasar a shekara mai zuwa, da kuma batutuwa da suka shafi tsaro, gami da yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.

Ta kara da cewa, a lokuta da dama matsayar da bababn malamin na kasar Iraki ya kan dauka a kan batutuwa daban-daban, sukan zama mafita, musamman ma yadda yake da karbuwa da kuma yadda al’ummar kasar ta Iraki take saurara masa, da kuma yadda yakan yi amfani da zurfin tunani da kuma duba maslahar al’ummar kasar kafin daukar kowane irin mataki da zai yi.

3922703

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: