IQNA

Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Isra'ila Da Wasu Larabawa Ba Falastinawa Ba

21:24 - September 16, 2020
Lambar Labari: 3485192
Tehran (IQNA) Bahrain da hadaddiyar daular larabawa sun rattaba hannu kan kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila ba tare da falastinu a cikin yarjejeniyar ba.

Gwamnatocin kasashen Bahrain da hadaddiyar daular larabawa sun rattaba hannu tare da firayi ministan Isra’ila kan kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila a fadar White House da ke birnin Washington na Amurka.

Dukkanin bangarorin uku sun rattaba hannu a kan abin da suka kira yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu, inda suka jaddada cewa za su ci gaba da yin aiki tare a tsakaninsu.

توافق نمایشی به کارگردانی ترامپ بدون ارانه راه‌حلی برای مساله فلسطین

Gwamnatin Amurka ce dai ta jagoranci rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, inda shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya jagoranci taron rattaba hannun, wanda kuma ya bayyana cewa kafin taron ya tattauna da sarkin Saudiyya Sda kuma yarimansa  ta wayar tarho, kuma sun nuna goyon bayansu kan hakan, kuma su ma za su biyo baya.

Trump ya ce ya bayar da umarnin a yanke duk wani tallafi da Amurka take baiwa Falastinawa, saboda ba su girmama gwamnatin Amurka.

توافق نمایشی به کارگردانی ترامپ بدون ارانه راه‌حلی برای مساله فلسطین

A nasa bangaren Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanya ya jaddada cewa, wannan yarjejeniya ba ta kunshi wani sharadi na janyewar Isra'ila daga wani wuri na Falastinawa da ta mamaye ba, kamar yadda kuma ba kunshi wani sharadi na dakatar da mamayar Isra'ila a kan yankunan falastinawa ba.

3923208

 

 

captcha