IQNA

22:08 - September 18, 2020
Lambar Labari: 3485197
Tehran (IQNA) Falastinawa sun shelanta ranar yaua matsayin ranar fushi domin nuna takaici kan yadda wasu gwamnatocin larabawa suke ha'intar su.

Jagororin kungiyoyin Falastinawa sun shelanta ranar yau Juma’a a matsayin ranar fushi ga dukkanin al’ummar Falastinu, domin nuna takaici kan yadda wasu daga cikin gwamnatocin larabawa suka mika kai ga yahudawan Isra’ila.

Rahotanni daga Falastinu na cewa, bayan sanarwar da jagororin kungiyoyin falastinawa suka bayar, a yau Juma’a al’ummar Falastinu suna gudanar da zanga-zanga da jerin gwano domin yin tir da Allawadai da gwamnatocin kasashen larabawa da suka kulla hulda da Isra’ila a hukumance kuma a bayyane.

Bayanin jagororin Falastinawan ya bayyana ranar yau Juma’a a matsayin ranar makoki, a kan aka bukaci Falstinawa da su daga bakaken tutoci a dukkanin yankunan Falastinawa, domin nuna bakin ciki a kan ha’inci na shugabannin larabawan da suka dauki wannan mataki.

 

 

3923613

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: