IQNA

22:41 - September 22, 2020
Lambar Labari: 3485208
Tehran (IQNA) Ilhan Umar ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin mutum mai tsananin nuna wariya a tsakanin al’umma.

Shafin yada labarai na Breitbart News ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai dangane da littafin da ta rubuta mai suna (Amurka haka take; tafiya ta daga neman mafaka zuwa wakilci a majalisa) ta bayyana cewa; ta yi kokari a cikin littafin nata ta bayyana kimar ‘yan adamtaka a matsayin ma’ani na rayuwa jama’a.

Ta ce; wannan shi ne abin ta sanya a gaba, kuma shi ne ya bata nasara a cikin lamurra da dama, amma kuma  a daya bangaren wannan bai kawar da kalubale da take fuskanta daga masu akidar wariya da kin wani jinsi na ‘yan adam ba.

Ilhan ta bayyana shugaban kasar Amuka mai ci a  yanzu Donald Trump, a matsayin daya daga cikin mutane masu tsananin nuna wariya da kyamar wani jinsi na mutane, ko dai saboda addini, ko kuma saboda launin fata ko kuma bangaranci, inda ta ce yana yin amfani da matsayinsa domin yada wannan mahanga tasa.

A cikin wasu kalamansa lokutan baya, Donald Trump yana bayyana Ilhan Omar a matsayin ‘yar gudun hijira da take neman musuluntar da Amurka, ya ce tana neman mayar da Amurka kamar kasarta Somali, a kan haka ya ce yana kira gare da ta koma inda ta tafito, kalaman da suka jawo ce-ce ku-ce a kasar ta Amurka.

 

3924626

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: