IQNA

Salami: Manufar Amurka A Gabas Ta Tsakiya Ba Ta Alhairi Ba Ce

22:35 - September 23, 2020
Lambar Labari: 3485212
Tehran (IQNA) Janar Husain Salami Ya bayyana cewa; manufar Amurka ita ce ci gaba da bautar da mutanen yankin gabas ta tsakiya.

Manjo Janar Husain Salami wanda ya gabatar da jawabi a yau Laraba a yayin bikin kaddamar da sabbin jiragen sama marasa matuki da jiragen sama masu saukar angulu ga rundunar ruwa a garin Bandar-Abbas, Ya bayyana cewa;“ Amurka ba za ta daina aiwatar da siyasarta ta shimfida ikonta akan kasashe ba, da hakan yake nufin bautar da su.”

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma yi ishara da shirin shugaban kasar Amurka na kashe shugaban kasar Syria, sanann ya kara da cewa; “ Wannan shi ne shugaban da yake da alaka da shugabannin larabawa masu alaka da Isra'ila, da hakan yake sa al’ummar musulmi na kin jininsu.”

Manja janar Salami ya kuma bayyana cewa; Iran ya sami nasarori masu yawa saboda juriyar da al’ummar Iran su ke nuna nunawa da kuma kyakkyawan jagoranci na jagora, don haka ba ta tsoron barazanar kasashe masu takama da karfi.

 

3924848

 

 

captcha