IQNA

Abbas: Gwagwarmaya Domin Kwatar Hakki Halastaccen Lamari Ne Ga Falastinawa

23:01 - September 26, 2020
Lambar Labari: 3485219
Tehran (IQNA) Mahmud Abbas shugaban falastinawa ya bayyana gwagwarmaya domin neman ‘yanci hakki ne na al’ummar Falastinu.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya bukaci wani taron kasa da kasa a farkon shekara 2021 mai zuwa kan rikicin Falasdinu da Isra’ila.

A jawabinsa na babban taron zauren majasar dinkin duniya, Mahmud Abbas, ya yi fatan taron zai samu goyan bayan da ake bukata domin samar da shirin zaman lafiya na gaskiya domin kawo karshen mamayar Isra’ila.

Abass ya ce, a ci gaba da tsokanar da take Isra’ila ta wargaza dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma da ita a shekarun baya, sannan kuma ta kore duk wani yunkuri na asamar da kasashe guda biyu.

Haka zalika Mahmood Abbas, ya soki matakin wasu kasashen larabawa na baya baya nan musamman Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrein na kulla alaka da Isra’ila a karkashin jagorancin Amurka.

 

3925314

 

 

 

 

 

 

captcha