Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa, Amurka tana kokarin dawo da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a cikin kasashen Iraki, Syria da kuma Lebanon.
A cikin wani jawabi da ya gabatar a daren jiya dangane da halin da ake ciki a kasar Lebanon kan batun cikas da ake samu wajen kafa gwamnati da kuma dalilan da suka jawo hakan, Sayyid nasrullah ya bayyana cewa, akwai hannun wasu kasashen ketare wajen yunkurin ganin an kassara kasar Lebanon tare da hana ta ci gaba.
Ya ce, a kwanakin bayan ya yi magana kan shirin Amurka na sake dawo da kungiyar Daesh a cikin kasashen Iraki, Syria da kuma Lebanon, amma wasu ‘yan siyasa akasar suka mayar da maganar abun izgili, wanda kuma abin da ya faru a cikin wannan makon kai harin da ‘yan ta’addan daesh suka yi a arewacin Lebanon ya tabbatar da hakan.
Ya ce manufar Amurka ta sake dawo da wadannan ‘yan ta’adda ita ce samo ma kanta dalili na ci gaba da wanzuwarta a gabas ta tsakiya, da sunan yaki da ta’addanci, wanda hakan ne kuma babban dalilin da yasa Amurka ta kashe Janar Qasem Sulamiani da Abu Mahdi Almuhandis, domin su ne suka kawar da Daesh a cikin Iraki da Syria, kuma a imanin Amurka matukar wadannan mutanen biyu suna raye ba za ta iya cimma wannan buri nata ba a gabas ta tsakiya.
3926306