IQNA

Kuwait Ta Jaddada Matsayinta Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Al'ummar Falastinu

23:40 - October 01, 2020
Lambar Labari: 3485236
Kuwait Ta Jaddada Matsayinta Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Al'ummar Falastinu
Tehran (IQNA) Sabon sarkin kasar Kuwait ya bayyana cewa gwamnati da mutanen kasar za su ci gaba da goyon bayan al-ummar Falasdinu.

Sarki Nawaf Al-Ahmad Aljabir Al-Sabah ya bayyana haka a ranar yau Alhamsi a lokacin da yake zantawa da Isma’el Haniyya shugaban kungiyar Hamas ta Falasdniya a yankin Gaza ta wayar tarho.

Sarkin ya kara da cewa kasar Kuwait zata ci gaba da muhimmanci ga al-amuran masu muhimmaci na al-ummar Musulmi, musamman al-ummar Falasdinu.

A na shi bangaren shugaban Hamas Isma’ila Haniyya ya yaba wa marigayi sarki Sabah Al-Ahmad Aljabir Assabah saboda tallafin da ya bawa al-amarin falasdinawa a shekarun da suka gabata.

A ranar Talatan da ta gaba ce sarkin ya rasu yana dan shekara 91 a duniya bayan rashin lafiya.

 

3926661

 

 

captcha