IQNA

Iran Ta Kirayi Bangarorin Azerbaijan Da Armeneia Da Su Yi Hattara Da Iyakokinta

22:43 - October 04, 2020
Lambar Labari: 3485242
Tehran (IQNA) Iran ta yi hannunka mai sanda ga dakarun kasashen Azerbaijan da Armeniya dake rikici a yankin Karabakh, da kada su yi gigin sanya kafa a cikin kasarta.

Gargadin na Iran na zuwa ne bayan da wasu makaman atilari suka fado a wasu kauyukan na Iran dake kan iyakoki.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran din ta fitar, ta ce ba zata lamunci keta iyakokinta ba daga dukkan bangarorin dake rikici, tare da bukatar bnagarorin su kwana da sanin lamuncihakan.

Bayanai da kamfanin dilancin labaren Iran na Irna ya fitar sun ce an samu yaro guda da ya jikkata sakamakon fadowar wani makamin atilari a kauyen Parviz Khanlou dake yankin Azerbaijan ya yamma, inda masana’antu da gidajen da dama suka lalace.

Iran dai na ci gaba da kira ga kasashen na Azerbaijan da Armeniya dasu kai zuciya nesa a kazamin fadan da suka kwashe kwanaki suka gwabzawa a yankin Karabakh, tare da cewa a shirye ta ke ta taimaka wajen shiga tsakanin bangarorin.

 

3926968

 

 

 

 

 

 

 

captcha