IQNA

Rouhani: Takunkuman Amurka Ba Su Sanya Iran Ta Zama 'Yar Amshin Shata Ba

23:07 - October 10, 2020
Lambar Labari: 3485261
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran ya bayyana cewar sabbin takunkumin da Amurka kan Iran wani aiki ne na ta’addanci.

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa bangaren bankunan Iran wani aiki ne na ta’addanci da kuma mugunta da nufin hana Iran sayen abinci da magunguna duk kuwa da annobar korona da ake fama da ita.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a a yammacin jiya Juma’a inda yace duniya ta shaida cewa wadannan matakai da Amurka take dauka sun saba wa dokokin kasa da kasa. Shugaban ya kara da cewa wannan mataki da Amurkan ta dauka yayi hannun riga da ‘yan’adamtaka musamman a wannan lokaci da ake fama da annbobar korona, don haka ya kirayi kungiyoyin da suke ikirarin kare hakkokin bil’adama da su yi Allah wadai da hakan.

Shugaban na Iran ya ce wadannan matakai da gwamnatin Trump ta Amurka take dauka kan Iran duk wani kokari na ganin ta dunkufar da al’ummar Iran, sai dai shugaba Rouhanin ya ce koda wasa wadannan matakan ba za su sanya al’ummar Iran mika wuya ba.

A shekaran jiya Alhamis ne Amurkan ta sanar da sanya sabbin takunkumin kan wasu bankuna da cibiyoyin kudi na Iran su 18 wadanda suke gudanar da ayyukansu a bangarorin ayyukan gona, samar da basussuka don gina matsugunnai musamman ga marasa abin hannu da sauran ayyukan na ci gaban kasa da taimakon al’umma.

 

3928219

 

 

captcha