IQNA

Kungiyoyin Gwagwarmaya A Iraki Sun Gargadi Amurka Kan Gaggauta Janye Dakarunta A Kasar

23:46 - October 11, 2020
Lambar Labari: 3485265
Tehran (IQNA) Kungiyoyin gwagwarmayar kasar Iraki za su dakatar da kai hare-hare kan sojojin Amurka don ba su damar ficewa daga kasar.

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce: Don girmama irin kyakkyawan aiki da kokarin da wasu masu kishin kasa suke yi wajen ganin an tsara yadda sojojin kasashen waje za su bar kasar, don haka kungiyoyin sun ce za su dakatar da hare-haren da suke kai musu, to sai dai sun ja kunnen Amurka kan abin da zai biyo baya matukar ta ci gaba da yaudarar da ta saba ko kuma jinkiri wajen kwashe sojojin na ta daga Irakin.

Har ila yau kungiyoyin sun ce matukar dai sojojin kasashen wajen ba su fice daga kasar ba, to kuwa za su dau mataki na gaba wanda shi ne fito na fito da sojojin da kai musu hare-hare a duk inda suke.

Tun dai bayan kisan gillan da Amurka ta yi wa tsohon babban kwamandan rundunar Kudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci Laftanar Janar Qasim Sulaimani da kuma mataimakin kwamandan dakarun sa kai na Hashd al-Sha’abi na Irakin Abu Mahdi al-Muhandis, kyamar Amurka ya ke karuwa a Irakin da kuma kiran da su fice daga kasar.

 

3928675

 

 

 

 

captcha