IQNA

22:59 - November 04, 2020
Lambar Labari: 3485336
Tehran (IQNA) an kori wani malamin jami’a a kasar Masar saboda yin wulakanci ga addinin muslunci

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, wani malami a jami’ar Iskandariyya a kasar Masar saboda yin wulakanci ga addinin muslunci, bayan da ya kawo batun batuncin da aka yi wa manzon Allah a Faransa.

Malamin yana tattauna wannan batu ne tare da dalibai a cikin aji, inda ya nemi yak are abin da jaridar Faransa ta yi an yin batunci ga manzon Allah da ma addinin muslunci, lamarin da ya fusata daliban nasa matuka, daga sai ya fice dga cikin ajin.

Ministan ilimi na kasar Masar Khalid Abdulgaffar ya bayar da umarini kan a kori malamin daga ikinsa, kuma a gudanar da bincike kan lamarinsa  a cikin sa’oi 48.

Wannan lamari ya bayyana ne bayan da daliban nasa suka watsa abin da ya faru a cikin kafofin sada zumunta na yanar gizo, inda hakan ya jawo fushin jama’a da dama  akasar, tare da yin kira da a hukunta shi.

 

 

3933263

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hukunta ، kafofin sada zumunta ، kasar Masar ، wulakanta ، addinin muslunci ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: