IQNA

22:44 - November 05, 2020
Lambar Labari: 3485338
Tehran (IQNA) kotun birnin Toronto na kasar Canada za ta saurari shari’ar mutumin da ya kashe wani musulmi ta hanyar daba masa wuka a birnin.

Shafin yada labarai na Toronto City News ya bayar da rahoton cewa, a yau ne kotun birnin na Toronto na da ke kasar Canada za ta koma zaman sauraren shari’ar mutumin da ya kashe wani musulmi ta hanyar daba masa wuka a masallacin Etobicoke.

An kashe musulmin ne mai suna Muhammad Islam Zafis dan shekaru 58 da haihuwa a kusa da gefen masallaci a ranar 12 ga watan Satumban da ya gabata, wanda kuma ya kasance daya ne daga cikin ammbobin kungiyar (International Musulims Organization).

Jami’an ‘yan sanda sun cafke mutumin da ya aikata wannan mummunan aiki, kuma sun gabatar da shi a gaban kuliya tun a cikin watan na Satumba, inda  a yau ne a ke ci gaba da sauararen shari’ar.

Jami’an ‘yan sandan birnin Toronto sun bayyana cewa, kwanaki 5 kafin ya aikata wannan kisa, ya yi wani yunkurin aikata wani kisan.

 

3933442

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: