IQNA

23:38 - November 13, 2020
Lambar Labari: 3485363
Tehran (IQNA) Isra’ila tana yin hanzari wajen ci gaba da yin gine-gine a cikin yankunan Falastinawa da ta mamaye.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana gaggauta gine-ginen da take yi a yankunan Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da suka mamaye, kafin sabon shugaban kasar Amurka karbi Iko.

Jaridar Haaretz ta haramtacciyar kasar ta bayyana cewa hukumomin gine-gine da kuma filaye a kasar suna gaggauta bada izinin gina sabbin wurare da kuma gaggauta kammala wadanda aka fara cikin watanni biyu da suka rage na sauya shugabanci a kasar Amurka.

Rahotannin sun kara da cewa akwai tsoron cewa zabebben shugaban kasar Amurka Joe Biden ba zai amince da haramtattun gine-ginen da HKI take yi a wadannan yankunan ba.

Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa zabebben shugaban kasar yana da hannu a dakatar da gine-ginen gidajen da aka yi a gwamnatin Obama, a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

 

3934866

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: