Shafin yada labarai na Sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, a jiya Juma’a an gudanar da sallar juma’a a masallacin haramin Makka mai alfarma, tare da daukar kwararn matakai na kiwon lafiya.
A yayin gudanar da hudubar juma’a an tarjamata zuwa harsuna daban-daban domin amfani masallata da suke wurin daga kasashe daban-daban.
Dalibai 80 daga jami’a sun halarci wurin domin yin hidima ga masallata da suka zo sallar juma’ a da kuma ziyara a masallacin harami.
An dauki matakin dawo da sallar juma’a ne bayan tabbatar da cewa an dauki matakan kiyaye kamuwa daga cutar corona, da kuma yada ta a tsakanin masallata
3935163